Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fasa zuwa taron G20 na ƙasashe masu ƙarfin masana’atu a duniya, sakamakon matsalar satar ɗalibai a ƙasar .
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce shugaban ya ɗauki matakin ne sakamakon halin da ake ciki a ƙasar na satar ɗalibai a makarantu.
A maimakon haka Shugaba Tinubu ya tura mataimakinsa Kashim Shettima domin ya wakilce shi a taron.
Tun da farko fadar shugaban ƙasar ta ce Tinubu ya ɗage tafiyarsa zuwa taron sakamakon sanin halin da ake ciki game da satar ɗalibai a Kebbi da masu ibada a jihar Kwara.
An tsara gudanar da taron ne a yau Asabar 22 ga watan Nuwamban 2025.









