Burkina Faso ta tsare jirgin sojin Najeriya kan keta sararin samaniyar ƙasar

Gwamnatin Burkina Faso ta ce an tilasta wa wani jirgin saman sojin saman Najeriya ɗauke da sojoji 11 sauka a ƙasar a ranar Litinin bayan da aka ce ya keta sararin samaniyar ƙasarta.

Wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin ƙasar ta ce jirgin sojan na ɗauke da ma’aikata biyu da fasinjoji tara a cikinsa kuma dukkansu jami’an soji ne.

Sanarwar ta ƙara da cewa, binciken da hukumomin ƙasar Burkina Faso suka gudanar ya nuna cewa jirgin ba shi da izinin shawagi a sararin samaniyar ƙasar.

Ƙungiyar AES ta yi Alla-wadai da lamarin a matsayin keta haddin kasar, tana mai cewa “ta yi suka da kakkausan lafazi kan keta sararin samaniyar duk wata ƙasa da ke cikin ƙungiyarta”.

Ƙungiyar, ta yi gargaɗin ɗaukar mataki kan duk wani jirgi da ya keta sararin samaniyar duk wata ƙasa da ke yankin ba tare da izini ba.

Ya zuwa yanzu dai babu wani bayani daga rundunar sojin saman Najeriya ko gwamnatin tarayya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com