Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta ƙaddamar da wani mummunan hari kan mayakan IS a arewa maso yammacin Najeriya.
“Dakarun Amurka sun ƙaddamar da hare-hare masu kyau,” in ji Trump.
Cibiyar sojin Amurka a Afrika daga baya ta ce an kai hare-haren ne a jihar Sokoto.
Read Also:
Shugaban ya zargi ƙungiyar da kai hari tare da kashe Kiristocin da ba su ji ba su gani ba a ƙasar.
A shafinsa na Social Truth, Trump ya wallafa da yammacin Alhamis cewa “a ƙaƙashin shugabancina, ƙasarmu ba za ta bar masu tsattsauran ra’ayin Musulunci sun girmama ba.”











