APC ta yi watsi da yunƙurin tsige Gwamna Fubara

Jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ta yi fatali da yunƙurin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar ke shirin yi.

Cikin wata sanarwa da APC ta fitar ta ce duk da cewa tana girmama cin gashin kan majalaisar dokoki, amma ba za ta amince da yunƙurin tsige gwamnan ba.

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ƙaddamar da yunƙurin sake tsige gwamnan da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, saboda zarginsu da laifukan da suka saɓa ƙa’idar aiki.

Jam’iyyar APC da ke mulkin jihar ta bayyana shirin da yunƙurin ”tayar da hargisti” a jihar.

APC ta kuma yi kira ga mambobin majalisar dokokin jihar su kauce wa duk wani yunƙuri da zai jefa jihar cikin rikicin siyasa.

A watan da ya gabata ne dai Gwamna Fubara ya koma APC bayan ficewarsa daga PDP.

Tun bayan zaɓen 2023, jihar – mai arzikin man fetur – ta faɗa rikicin siyasa sakamakon saɓanin da gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya samu da ministan Abuja, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Nysome Wike.

Ricikin ya ci gaba da ƙamari, lamarin da ya kai ga shugaban ƙasar, Bola Tinubu ayyana dokar ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da Gwamnan Fubara har na tsawon wata shida a shekarar da ta gabata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com