Gwamnatin Najeriya ta dakatar da tsare-tsare da za a yi amfani da su wajen aiwatar da sabbin dokokin haraji, tana mai kafa hujja da wasu rashin tabbas kan matakan ƙarshe da aka bijiro da su cikin sabuwar dokar.
Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan tsarin harajin, Taiwo Oyedele ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Legas, yana mai cewa akwai nazarce-nazarce da ya kamata a kammala bibiya kafin fara aiwatar da dokar.
Read Also:
Oyedele ya ce tuni ya shaida wa hukumomin da ke da ruwa da tsaki a ɓangaren haraji su dakata da duk wani aiki da ya shafi wannan doka.
Dokar haraji ta Najeriya, wadda ta fara aiki a ranar 1 ga Janairu, ta fuskanci suka bayan zargin cewa anyi sauye-sauye da majalisar dokokin ƙasar ta amince da su, akwai ɗungushe a ciki.
Sai dai Oyedele ya nuna damuwa kan yadda wannan mataki ke fuskantar caccaka, yana mai danganta hakan da yaɗa labaran ƙarya da nufin kawo cikas ga sabon tsarin harajin.
Ya ce yadda aka riƙa yamaɗiɗin labaran ƙarya a bara, hakan ya sanya Najeriya yin asarar Naira tiriliyan 4.6 a rana guda cikin watan Nuwamba.










