Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta fara bincike kan wani mummunan kisa da ya auku a unguwar Dorayi Chiranchi dake jihar Kano a ranar asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ba a san ko su wane ba sun shiga gidan Haruna Bashir, inda suka kai hari kan Fatima Abubakar mai shekaru 35 da ’ya’yanta shida, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsu.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya faru ne inda maharan suka shiga gidan ba tare da an gano su ba, suka aikata wannan ta’asa kafin su tsere daga wurin.
Maƙwabta sun ce sun farga ne da jin ihun mutane da kukan neman taimako, amma kafin a kai dauki, an riga an yi mummunan lahani.
Read Also:
Waɗanda abin ya rutsa da su sun haɗa da Fatima Kabir, matar gidan mai kimanin shekaru 35, sai babbar ‘yarta Maimuna Haruna da ƙanwarta. Aisha Haruna da ƙannenta maza Bashir da Abubakar, sai kuma jariri wanda ake goyo wanda aka jefa shi a rijiya bayan an kashe shi.
Jami’an tsaro sun isa wurin bayan samun rahoton faruwar lamarin, inda suka killace yankin domin fara bincike.
An kuma kwashe gawarwakin mamatan zuwa asibiti domin tantancewa da kuma shirya musu jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Al’ummar yankin sun nuna matuƙar alhini da damuwa kan wannan lamari, inda da dama ke kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara matakan tsaro, domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Hukumar ’yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta fara bincike mai zurfi domin gano waɗanda suka aikata laifin.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen cafke masu hannu a wannan aika-aika.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wanda aka kama, yayin da bincike ke ci gaba. Al’umma na ci gaba da nuna alhini da jimami, tare da addu’a ga mamatan da kuma fatan ganin adalci ya tabbata.










