Kisan gilla – Ƴansandan jihar Kano sun kama wadanda ake zargi da ƴaƴanta

Rundunar ƴan sanda jihar Kano ta tabbatar da kama mutum uku da take zargi da aikata kisan gilla ga wata mata da ƴaƴanta 6 a unguwar dorayi Chiranci dake jihar.

Kakakin Rundunar CSP Abdullah Haruna kiyawa ne ya tabbata da hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar a safiyar Lahadi.

Sanarwar ta ce dakarun rundunar sun kama Umar Auwalu mai shekara 23 dan unguwar sabuwar Gandun dake Kano da Isyaku Yakubu wanda aka fi sani da Chebe dan unguwar Sagagi sai kuma Yakubu Abdul’aziz wanda ake kira da wawo Mai kimanin shekaru 21 dan unguwar sabon gida Sharada.

Wanda ake zargi da jagorantar wannan kisa wanda dan uwa ga Matar Auren da aka hallaka ya amsa laifinsa wanda yace su suka aikata kisan kan da aka yi ta hanyar kone Wasu matan aure biyu a unguwar tudun Yola dake jihar Kano.

Rundunar ta ce ta samu makamai da suka haɗar da hira, Adda da kuma kuma wasu kuɗi da suka yi fashinsu a lokacin, sai kuma muggan makamai da yanzu haka ake bincike akansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com