Rundunar Ƴansandan jihar Nasarawa ta sami nasarar tserar da wasu mutane 17 da ake kan hanyar safararsu daga jihar yayin wani binciken ababen hawa da suka gudanar a ƙaramar hukumar Karu ta jihar.
Wannan na cikin wata sanarwar da rundunar ƴansandan ta fitar, wadda ta ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata da misalin ƙarfe 5 da mintuna 50 lokacin da jami’anta ke tsaka da binciken ababen hawa a dai dai Mararaba inda suka ci karo da motar ƙirar Volkswagen Sharon mai lamba SHD 253 YU maƙare da mutanen su 17.
Sanarwar ta ci gaba da cewa bayan dogayen tambayoyi ne suka gano cewa babu gaskiya a tare da matuƙin motar wanda aka bayyana sunanshi da Nanle John mai shekaru 36, da ke ɗauke da fasinjan su 17 galibinsu ƙananan yara da suka ƙunshi Maza 11 da Mata 6 da ke a tsakanin shekarun 10 zuwa 19.
Read Also:
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin kakakin rundunar ƴansandan jihar ta Nasarawa Ramhan Nansel tun farko sun yi zargin babu gaskiya a cikin yanayin bulaguron fasinjan da ke cikin motar hakan ya sanya su tsananta bincike inda suka gano cewa safarar yaran ake shirin yi.
Daga bayanan da aka samu daga mutanen, sun shaidawa rundunar ƴansandan cewa an ɗebo su ne daga yankin Shendam na jihar Pulato kuma suna kan hanyar zuwa Kayama ne a jihar Kwara inda za a damƙa su a hannun wasu mutum mai suna Umaru da ya yi alƙawarin samar musu aikin noma a ƙauyensu.
Duk ƙoƙarin da rundunar ƴansandan ta yi wajen tuntuɓar iyayen yaran da ke cikin motar yaci tura lura da yadda aka gaza samunsu a lambobin wayar da aka baiwa jami’an.
Mr Nansel ya ce tuni suka tsare ilahirin yaran su 17 yayinda Kwamishinan ƴansanda na jihar Shetima Mohammed ya umarci tsananta bincike don gano masu hannu a safarar tare da sada yaran da iyayensu.











