Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin jakadu hudu, daga cikin 68 da Majalisar Dattawa ta amince da su a watan Disamban 2025.Tinubu ya tabbatar da nadin Ayodele Oke a matsayin jakadan da aka nada a Faransa, da kuma Lateef Are a matsayin jakadan da aka nada a Amurka.
Shugaban Najeriya ya kuma tabbatar da nadin Amin Dalhatu, tsohon jakadan Korea ta Kudu, a matsayin babban kwamishina da aka nada a Birtaniya.
Read Also:
Usman Isa Dakingari Suleiman, tsohon gwamnan Kebbi, shi ne jakadan da aka nada a Turkiyya,ƙasar da Shugaba Tinubu zai fara ziyara a mako na sama.
A cikin wata sanarwa da ya aike wa Ma’aikatar Harkokin Waje, Shugaba Tinubu ya bukaci ma’aikatar ta sanar da gwamnatocin kasashen hudu game da nadin jakadun, bisa ga tsarin diflomasiyya.
Mai baiwa shugaba Tinubu shawara kan dabaru da hulda da manema labarai Bayo Onanuga,ya jaddada manufar shugaba Tinubu na ganin Najeriya ta shiga sahun manyan ƙasashe a fanin diflomasiyya.











