Shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da yunƙurin juyin mulki a watan Oktoban bara

Shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da fuskantar yunƙurin juyin mulki ga gwamnatin ƙasar a kwanakin baya, wanda ta ce ta gano hakan ne bayan tsananta bincike kan wasu jami’anta da ta zarga da rashin ɗa’a inda sakamako ya tabbatar da cewa tabbas sun yi shirin kifar da gwamnatin ƙasar.

Tun a watan Oktoban 2025 ne, shalkwatar tsaron Najeriyar ta sanar da kame wasu manyan sojoji 16 bayan zarginsu da saɓa dokokin aiki, kodayake a wancan lokaci ta ƙi amsa zargin cewa sun yi shirin kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ne.

A wancan lokaci wata kafar labarai a Najeriyar ta ruwaito cewa sashen tattara bayanan sirri na Najeriyar ya kame Sojojin masu muƙamai daga kyaftin zuwa Birgediya Janar su 16 lokacin da suke gudanar da wani taron sirri kan shirin kifar da gwamnati.

Kafar a wancan lokaci ta alaƙanta matakin soke faretin ranar 1 ga watan Oktoba da yunƙurin juyin mulkin, sai dai a wancan lokaci daraktan yaɗa labarai na shalkwatar Birgediya Tukur Gusau ya yi watsi da zargin wanda ya ce yunƙuri ne na haddasa yamutsi a tsakanin jama’ar ƙasar.

Sai dai da ya ke ƙarin haske kan lamarin a wannan Litinin, Manjo Janar Sama’ila Uba ya ce bayan dogon bincike irin na Soji kan Jami’an, ya tabbata suna kitsa shirin kifar da gwamnatin ta Najeriya.

A cewar Manjo Sama’ila Uba, mutanen su 16 za su gurfana don amsa tuhuma kan wannan zargi bisa tanadin dokokin aikin Soji na Najeriya, yayinda ya ce za a yi hukuncin ne a fayyace bisa tsantsar gaskiya da adalci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com