Najeriya ta sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar babban layin lantarkin ƙasar a ranar Talata,
Wannan shi ne karo na biyu da babban layin wutar ke fuskantar irin wannan matsala a shekarar 2026 wanda ya haifar da katsewar wutar lantarki a fannoni da dama na ƙasar.
Layin wutar ya fara lalacewa ne a ranar Juma’a da ta gabata.
Masana da hukumomi sun danganta lalacewar da tangarɗar na’ura da rashin cikakken gyare-gyare da kulawa ga manyan layukan wuta.
Bincike ya nuna cewa dukkanin tashoshin samar da wutar lantarki 23 da ke haɗe da babban layin sun daina aiki gaba ɗaya.
A halin yanzu, babu cikakken bayani kan abin da ya janyo wannan lalacewa.











