Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa mayaƙan Iswap sun kai hari kan sojojinta a garin Sabon Gari da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar.
Rundunar ta ce an kai harin ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, kuma ta ƙara da cewa mayaƙan sun yi amfani ne da jirage marasa matuƙa.
A sanarwar da rundunar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar wasu sojoji da ba ta bayyana adadinsu ba.
Mai magana da yawun rundunar, Sani Uba, ya ce an kai harin ne a wani sansanin soji da ke yankin, amma ya ce, “sojojin sun daƙile harin, sannan komai ya lafa.”
A sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, Mr Uba ya ce kafin harin, sojojin na Najeriya sun kai hare-hare a yankin Bulo Dalo, inda a cewarsa suka kashe mayaƙa 12, sannan suka kai wani harin a garin Garno shi ma na jihar ta Borno duka a ranar Laraba, inda a cewarsa a can ma suka kashe mayaƙan guda shida. Ya ƙara da cewa sojojin sun ƙwace makamai da alburusai.











