Yadda Iyalan Sheik Agaka Suka Bawa Iyalai Na Ilimin Addinin Musulunci, “Sulu Gambari”

Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, ya bayyana Marigayi Dr. Abdulhameed Shuaib Agaka matsayin mai kyakkyawan halaye da riko da addini.

Sheik Agaka, Mahaifi ga mawallafin jaridar PRNigeria kuma babban mai tace labarai, Yusha’u Shuaib, ya rasu a ranar Asabar, yana da shekaru 77 a duniya.

Agaka fitacce malamin Addinin muslunci kuma babban limamin garin Agaka dake masarautar Ilorin ta Jihar Kwara, ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa dake garin, bayan yayi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Haka zalika yana da digirin digirgir a fannin falsafa, an haife shi a cikin dangin Imam Shuaib Saeed, wani mashahurin malami masanin Al’kurani kuma jagoran addini musulunci.

Mai Martaba sarkin Ilorin Sulu Gambari ya bayyana matukar kaduwarsa bisa ga rasuwar mahaifin mawallafin jaridar ta PRNigeria, yayi da ya karbi bakuncin tawagar Iyalan marigayin, a fadarsa, a ranar litinin.

Mai martaba sarkin ya kuma jajantawa tawagar iyalan marigayin bisa jagorancin Dawudu Agaka, Alh. Hanafi Folorunsho Kawu, da daukacin  iyalan Malamin bisa rashin da suka yi na hazaki, kuma cikakken Mutum mai adalci marashin aibi.

Sarkin bayyana cewa Al’ummar jihar kwara da kasa baki daya sunyi gagarumin rashi na malamin Addini da baza a iya misalta rashin ba.

Sarkin na Ilorin ya kara da cewa Iyalan Sheik Agaka, na da alaka da masu yawon yada addinin Musulunci “masu wa’azi” tsawon shekaru da dama a Nijeriya, kasancewar marigayu Abdulhameed ya kasance daya daga cikin manayan malaman addinin muslunci da masarautar ta samar.

Dr. Sulu Gambari, yace ya amfana matuka da wa’azin sheik Abduhameed, inda yace mahaifiyar sa ta kuma shafe shekarunta tana karatu al’kurani a wajen Sheik Agaka.

Tun bayan samun labarin mutuwar Sheik Agaka manayan malamai gami da masu rike da sarautun gargaji, da ‘yan takarda sun nuna kaduwar su matuka tare da Addu’ar Allah yayi masa rahama yasa Aljanna ce makoma ya kuma inganta abinda ya bari.

By PRNigeria

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 17 hours 42 minutes 43 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 24 minutes 8 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com