Majalisar wakilan Nijeriya ta yi zargin cewa an sace sama da Dalar Amurka Biliyan 10 na danyen man fetur, ta hanyar badakalar tallafin Man wanda kamfanin man fetur na kasar NNPC da sauran masu ruwa da tsaki a kamfanin su ka yi.
Don haka majalisar ta kafa wani kwamitin wucin gadi da zai binciki tsarin tallafin man fetur tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021 da ga kamfanin na NNPC ya yi.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Dan majalisa mai wakiltar Edo Sergious Ogun ya shigar gaban majalisar a ranar laraba a birnin tarayya Abuja.
Read Also:
Ta cikin kudirin nasa, Mista Ogun yace an sanar da shi cewa a shekarar 2002, kamfanin na NNPC ya sayi danyen mai a farashin kasuwannin duniya, wanda ya kai ganga 445,000 a ko wacce rana.
Ya kara da cewa anyi hakan ne domin bada damar samar da man da ake amfani da shi a cikin gida, amma abin damuwar shine yadda a shekarar 2002 matatun man Nijeriya ke samar da ganga 445,000 a kowacce rana.
Sai dai kuma yace daga bisani karfin matatun ya ragu zuwa sifili sakamakon rashin inganci da kuma zargin cin hanci da rashawa ga masu ruwa da tsaki ya durkusar da fannin.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 38 minutes 2 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 19 minutes 27 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com