Home DUNIYA Amurka na Dari-Darin Shiga Tattaunawar Shirin Nukiliyar Iran

Amurka na Dari-Darin Shiga Tattaunawar Shirin Nukiliyar Iran

Kasar Amurka tayi watsi da duk wani yunkuri na sake shiga tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran nan kusa, abinda ake gani zai dakushe fatan da ake da shi  na kulla sabuwar yarjejeniya akan wadda akayi a shekarar 2015.

Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar John Kirby yace ba wai basa bukatar ganin an aiwatar da yarjejeniyar bace, sai dai a halin yanzu basu ga wata hanyar kulla ta ba a nan kusa.

Kirby yace abinda ke gabansu yanzu shine daukar mataki akan kasar Iran saboda yadda take murkushe masu zanga zangar adawa da mutuwar Mahsa Amini, matashiyar da aka samu da laifin kin sanya hijabi a ranar 16 ga watan Satumba.

Mai magana da yawun fadar shugaban yace har yanzu shugaba Joe Biden na nan kan matsayinsa cewar ba zai taba barin kasar Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Zanga zanga ta barke a sassan kasar tun bayan mutuwar Amini, abinda ya kaiga arangama tsakanin Yan Sanda da masu adawa da matakin da jami’an tsaro suka dauka, abinda ya kaiga mutuwar mutane sama da 100 da kuma kama wasu sama da 100 da tuni aka gurfanar a gaban shari’a.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya zargi Amurka da kawayenta da tinzira masu zanga zangar domin jefa kasar cikin tashin hankali, yayin da kasashen Turai suka amince da wani shirin kakabawa kasar takunkumi akan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp