Home DUNIYA Rundunar Sojin Benin ta dakile wani harin Ta’addanci a Arewacin kasar

Rundunar Sojin Benin ta dakile wani harin Ta’addanci a Arewacin kasar

Rundunar sojin Jamhuriyar Benin ta yi nasarar dakile wani hari da ‘yan ta’adda suka shirya kai wa yankin arewa maso yammacin kasar, wanda bayanai ke cewa ‘yan ta’addan sun kitsa yadda za a kai harin ne daga makwabtan kasar wato Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso.

Sanarwar da rundunar sojin ta Benin ta fitar ta ce yayin dakatar da harin dakarun soji sun yi nasarar hallaka ‘yan ta‘adda 8, yayinda da dama suka tsere da munanan raunuka.

Wasu alkaluma na nuni da cewa rundunar Sojin ta Benin ta yi nasarar dakile hare-haren ta’addanci har sau 12 daga bara zuwa yanzu, dai dai lokacin da barazanar tsaro ke ci gaba da tsananta a kasashen yankin Sahel sakamakon yadda kungiyoyin ‘yan ta’adda masu alaka da Al Qaeda da kuma IS ke ci gaba da yawa bisa ikirarin aikata jihadi.

Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in yada Labarai na rundunar Sojin ta Benin, Ebnezer Honfonga ta ce da misalin karfe 12 na daren jiya ne sojojoji suka wargaza shirin ‘yan ta’adda na shiga kauyen Materi, da nufin kaddamar da jerin hare-hare.

Sai dai kuma bayan da rundunar Sojin ta samu bayanai sirri ne ta afka musu ta hanyar yi musu kwantan bauna, duk da dai sun yi yunkurin mayar da martani ta hanyar tashin bama bamai da harbe harbe.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp