Home Labarai Gwamnatin Jihar Zamfara ta Rufe wasu Yankuna a Jihar Saboda Tsaro

Gwamnatin Jihar Zamfara ta Rufe wasu Yankuna a Jihar Saboda Tsaro

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta ɗauki matakin dakatar da kowace irin hada-hada a wasu yankunanta da ke fama da matsalar tsaro.

wannanna kunshe ne ta cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Juma’a, ta ce ta lura da yadda ake samun taɓarɓarewar tsaro ta hanyar sace-sacen al’umma a kauyuka da kuma kan wasu hanyoyin jihar.

A saboda haka sanarwar ta ce gwamnati ta kulle,  ƙananan hukumomin Anka da Bukuyum da kuma Gummi ɗungurungum.

Sauran kauyukan da kullewar ta shafa su ne Ƴarkofoji, da Birnin Tudu, da Rini, da Gora Namaye, da Janbako, da Faru, da Boko da kuma Mada.

Sanarwar ta kuma ce daga yau an rufe kasuwannin Danjibga da Bagega, Bugu da ƙari an dakatar da zirga-zirga kan hanyoyi da suka hadar da Colony zuwa Lambar Boko, Bakura zuwa Lambar Damri, Mayanchi zuwa Daki Takwas har zuwa Gummi, Daki Takwas zuwa Zuru, Kucheri zuwa Bawaganga zuwa Wanke, Magami zuwa Dangulbi sai kuma  Gusau zuwa Magami

Gwamnati ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu ba tare da wani cikas ba.

Ta kuma ce ta bai wa jami’an tsaro umurnin ɗaukan mummunan mataki kan duk wanda aka samu da laifin karya dokar.

jihar Zamfara na  guda cikin jihohin  Arewa maso yammacin Nijeriya da matsalar tsaro kekara karama sakamakon  ƴanfashin daji da ta fi kassarar jihar dama yankin.

PRNigeria Haus

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp