Wasu rahotanni na bayyana cewa akalla mutane 3 sun rasa rayukansu, sannan da dama sun jikkata sakamakon wani hari da aka kai da mota makare da bama-bamai da kuma harbe-harben bindiga kan wani otel da ke birnin Kismayu na kasar Somalia.
An fara jin karar harbe-harben bindiga jim kadan da fashewar bama-bamai da ke cikin motar wadda ta yi karo da babban kofar shiga cikin otel din na Tawakal, yayin da mayakan Al-Shebab masu alaka da Al-Qaeda suka dauki alhakin kaddamar da farmakin.
Rahotanni na cewa, an kai farmakin ne a daidai lokacin da ake kan gudanar da wani taro a otel din kan yadda za a murkushe mayakan na Al-Sshebab a kasar ta Somalia.
Read Also:
Har yanzu dai kungiyar ta Al-Shebab na rike da ikon wasu yankuna na birnin na Kismayu mai cike da hada-hadar kasuwanci a yankin kudancin Somalia.
Sojojin kasar sun yi nasarar fatattakar mayakan na Al-shebab daga birnin a shekara ta 2012, birnin da ke samar wa mayakan kudaden shiga domin sayen makamai.
Ko a shekara ta 2019, sai da mayakan suka kaddamar da makamancin wannan harin da ya kashe mutane 26 a Kismayu.
Har yanzu dai mayakan Al-Shebab ba su daddara ba a yunkurinsu na ganin sun kifar da gwamnatin Somalia domin kafa irin tasu gwamnatin, yayin da suka kashe dubban ‘yan kasar a jerin hare-haren da suka kaddamar cikin shekaru 10.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 6 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 48 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com