Home DUNIYA Sarki Charles na III ya tabbatar da Rishi Sunak Matsayin Firaministan Birtaniya

Sarki Charles na III ya tabbatar da Rishi Sunak Matsayin Firaministan Birtaniya

Sarki Charles na III ya  tabbatar da Rishi Sunak matsayin Firaministan Birtaniya, kuma bayan tabbatarwar ya sha alwashin gyara kurakuran da aka tafka wadanda suka kai kasar ga fadawa halin matsananciyar matsalar tattalin arziki.

Sunak mabiyin addinin Hindu mai shekaru 42 wanda Sarki Charles na 3 ya tabbatar da shi a matsayin Firaminista da misalin karfe 11 da mintuna 15 na safiyar yau talata, shi ne Firaminista na 3 da kasar ta gani cikin shekarar nan.

Wannan ne dai nadi na farko da Sarki Charles na 3 ya jagoranta la’akari da cewa Sarauniya Elizabeth ce ta tabbatar da nadin Liz Truss kwanaki kalilan gabanin mutuwarta.

Jim kadan bayan tabbatar da shi, Rishi Sunak ya ce aiki na farko da zai sanya a gaba shi ne samar da sauye-sauye don gyara ga kura-kuren da aka tafka cikin makwanni 7 na mulkinta Truss lamarin da ya durkusar da tattalin arziki.

A cewarsa baya zargin Truss kuma matakan da ta dauka ba gazawa ba ce, haka zalika bada mummunar manufa ta samar da sauye-sauyen da suka illa ga tattalin arziki ba, hasalima tsari ne mai kyau sai dai sun juye zuwa matsala ne saboda halin da Duniya ke ciki.

Yayin jawabinta na ban kwana Truss ta yiwa Sunak fatan alkhairi da kuma fatar warwarewar matsalolin da suka dabaibaye sashen tattalin arzikin kasar wanda ya jefa jama’a a halin matsin tattalin arziki.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp