Gwamnatin mulkin Sojin Mali ta mayar da ‘yan sandan kasar karkashin rundunar sojojinta, a kokarin da take yi na murkushe ‘yan ‘ta’adda masu ikirarin Jihadi, wadanda suka shafe shekaru akalla 10 suna addabar sassan kasar.
Read Also:
Gwamnatin sojin kasar ta Mali ta ce matakin zai ba ta damar jibge ‘yan sandan a yankunan da sojoji suka kwato daga hannun ‘yan ta’adda, domin tabbatar da tsaron jama’a da dukiyarsu, da kuma dakile duk wani yunkuri na masu ikirarin jihadi ko ‘yan tawaye sake mamaye yankunan da suka subuce musu.
Majalisar zartaswar kasar ta rikon kwarya ce kuma ta CNT wadda sojojin da suka yi juyin mulki suka kafa ta zartar da dokar baiwa jami’an tsaro na ‘yan sanda kayan aikin sojoji mako guda da ya gabata.
Sai dai tun kafin amincewa da aiwatar da matakin mayar da su karkashin rundunar sojoji kungiyoyin ‘yan sandan suka soki manufar da suka bayyana a matsayin shawarar da bangare daya yayi gaban kansa wajen zartaswa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 32 minutes 7 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 13 minutes 32 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com