Asusun tallafawa da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) zai bayar da tallafin jin kai ga yara 21 da aka ceto a Katsina.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin UNICEF Samuel Kalu ya fitar a ranar Talata.
Mista Kalu ya ce kulawar zata taimaka wa yaran wajen magance matsalar da kuma sake shiga cikin al’umma.
Idan dai za’a iya tuna anyi garkuwa da yaran ne masu shekaru 16 zuwa 21 a ranar 30 ga watan Oktoba a wata gona da ke Mairuwa a karamar hukumar Faskari ta Katsina.
Wadanda abin ya shafa sun hadar da ‘yan mata 17 da maza hudu, wadanda aka sami nasarar kubutar da su bayan sun kwashe kwanaki shida.
Read Also:
“UNICEF na maraba da labarin sakin yara 21 da aka sace a wata gona da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya,” in ji hukumar ta UN.
“Muna yabawa hukuma kan matakin da ta dauka na sako yaran da aka yi garkuwa da su a ranar Asabar da ta gabata.
Sakin dukkan yaran 21 da aka sace, labari ne mai dadi a gare mu duka iyaye, masu kulawa, shugabannin al’umma, da kowa da kowa.”
Sanarwar ta kara da cewa, tun da farko bai kamata a yi garkuwa da wadannan yaran ba, domin babu wanda ya kamata a yi garkuwa da su, musamman kananan yara, ko kuma tashe-tashen hankula.
UNICEF ta kuma bayyana cewa, za ta tallafa wa ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Katsina don tallafa wa yaran da aka kubutar da su “don taimaka su murmure daga halin da suke ciki da kuma komawa cikin al’umma.”
NAN
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 10 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 52 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com