RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da ‘Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta’azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja.

RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da ‘Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta’azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja.
DAGA: Abbas Badmus da Kabir Abdulsalam
FASSARA: Rabiu Sani Hassan
A shekarar 2018 da Abdulrahman Yusuf ya baro garin Damboa, fitacciyar karamar hukuma a jihar Borno zuwa birnin tarayya Nijeriya Abuja, sakamakon matsalar ayyukan mayakan boko haram da na ISWAP.
Cikin kankanin lokaci, ya zauna a babban birnin kasar kuma nan da nan ya fitar da tunanin da yake ciki na irin kisan gilla da ‘yan ta’adda suka yi wa al’ummarsa da sauran yankunan Arewa maso gabas
Domin tsayawa da kafar sa, Yusuf mai kimanin shekaru 33 a duniya, a lokacin ya sayi babur, wanda zai ke neman taro da kwabo.
Bayan mallakar babur din yana amfani dashi wajen kasuwanci wato dai ‘Achaba’ babur din ya taimaka masa wajen rike kansa da iyalansa da suka yi gudun hijira, zuwa birnin Abuja.
Amma fa wannan ya kasance kawai na tsawon shekaru biyu ne, har zuwa watan Yunin 2021. Tun daga wannan lokaci, rayuwa ta sauyawa Yusuf.
A baya-bayan nan, makomar matashin dan gudun hijira daga jihar Borno ta shiga watangaririya, tun daga lokacin daga aka jefa aikin sa cikin halin ni’yasu, idan ba’a dauki matakin lura da Yusuf ba, akwai yiwuwar cewa zai iya shiga cikin bata gari domin aikata laifuka saboda mawuyacin halin da uake ciki.
Dalili: Ma’aikatan Babban birnin tarayya Abuja, FCT karkashin hukumar dake lura da titunan Birnin ta DRTS, ta kwace babur dinsa a watan Julin 2021,
An ‘kone’ Babura 1,500 da aka kwace
Amma hukumar ta DRTS bata tsaya nan ba, ta kone a kalla babu 1,500 wanda ta kwace tsakanin watan janairu zuwa Julin 2021; wanda akwai na Yusuf a ciki.
Idan aka lisafta Naira dubu 400,000 akan ko wanne babur, yanzu Babura 1,500 da aka lalata sun tashi a naira 600,000,000.
PRNigeria ta tattaro cewa an kama wasu baburan ‘Achaba’ 1,500. Wanda da alaman an kamasu ne a ‘yan tsakanin nan, kaga nan ba da jimawa ba zasu fuskanci kwatankwacin halin da dan uwansu ya shiga.
An kara latata wasu baburan Achaba 1,500
Bajimawa sabon daraktan hukumar ta DRTS, Mista Abdullateef Bello, ya bayyana cewa Karin Babura 1,500 da aka kwace hannun masu aikin Achaba a birnin a lalata su.
Wannan shine rukuni na biyu na baburan ‘Achabar’ da aka lalata karkashin hukumar DRTS, cikin watanni 15.
Yace “baburan ana amfani da su ne domin harkokin kasuwanci, wannan ne yasa aka lalata su bayana matukan su sun karya dokokin tuki a birnin.
A shekarar tada gabata wanda Bello ya gada Wadata Bodinga, a watan disamba 2021, da kansa ya sanya idanu domin kona Babura na farko da aka kama.
Bello, ya kara da cewa “kamar yadda mukayi shekarar data gabata, wadannan Babura da aka kwace na zaman jiran lokacin da za’a kone/lalata su.
Ya kuma bayyana cewa “idan aka gudanar da wannan aiki, a birnin tarayyar kadai an lalata Babura dubu 3,000 na wadanda ke amfani da su a cikin kwaryar birnin cikin watannin 16, wand aya kara yawan matasa da rayuwar su ta dogara kacokan a wannan aiki na Achaba.
Dokar Aikin ‘Achaba’ a birnin Tarayya Abuja
PRNigeria ta tattaro cewa hukumar babban birnin tarayya, FCTA, a shekarar 2015 ta fidda wata sanarwar dake umartar matuka baburan na ‘Achaba’ dake Abuja da su daina gudanar da ayyukan su kan manyan titunan dake tsakiyar birnin.
Yadda dokar ta yamutsa hazo
Ko da yake dokar nada matukar amfani, amma masu kalubantar ta na jefa ayar tambaya kan yadda gwamnati da hukumomin da ke da alhakin dokar, ta yadda suka kirkiri dokar ba tare da jin tausayin na kasaba ko halin da zasu sanya wadanda suka sanyawa dokar.

Sun yi da halin da matuka Babura da suka karya irin wannan doka ke ciki, wanda kama yayi aci tarar sub a wai a kune baburan ba, amma sai mayuka suka wayi gari ana kune musu Babura.
Suna kalubalantar hukuncin, kan domin matuka baburan sun karya dokokin hanyoyi a birnin, mai zai saka a lalata musu Baburan da suke amfani dasu domin gudanar da rayuwar su ta yau da kullum, wannan rashin adalci ne.
Kamar dai motoci, suma baburan idan akayi amfani da su wajen sana’ar ‘Achaba’ suma suna tallafawa wajen habaka tattalin arziki, da kuma ragewa mutane radadi wajen rage musu yin tattaki ko tafiyar kafa.
Haka kuma, samun matasan dake gudanar da sana’ar ta Achaba yana da matukar muhimmancin wajen hana aikata laifuka a duk duniya.
Wani binciken wata kungiya ya bankado cewa aikata lafuka ya karu a birnin Abuja da kashi 62 cikin dari (60%) a cikin shekaru 3.
Sana’ar Achaba a India
Bincike ya nuna cewa a kasar Indiya kasar dake da yawan Babura miliyan 37 (kasa data fi kowacce kasa yawan sa a duniya) ba’a murkushe sub a, duk laifin da masu amfani dashi ke aikatawa.
Saboda mayar da miliyoyin matasan dake sana’ar Achaba marasa aikin yi, kasar ta amince da hukuncin cin tara mai yawan gaske da zaman gidan yari, ga masu keta dokar Ababan hawa a kasar dake yankin Asiya.
Abinda Matakain Vio Ya Haifar Kan ‘Yan Achaba
Kamar yadda akayi tsammani, binciken PRNigeria ya nuna cewa matuka baburan na Achaba, wadanda suka rasa aikin su sakamakon kwace babu da DRTS, wadanda akafi sani da VIO suka yi, tare da murkushe Babura, sun rungumi aikata manayan lafuka.
Sukan aikata laifuka daban-daban wanda ke kara ta’azzara rashin tsaro a Abuja.
Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da rashin aiki yi ga matasa a babban birnin tarayya Abuja ke kara karamari, inda ake samun yawaitar fashi da makami, fashi da makami, ‘yan fashi da makami, da ayyukan garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Duk da haka, ya dace a nuna cewa matsalar rashin aikin yi ba ta dawata matsala a birnin Abuja.
A wani taro daya gudana baya-bayannan, shugaban bankin raya Afirka na AfDB Akinwummi Adesina, ya koka da yadda ‘yan nijeriya ke fama da matsalar rashin ayyukan yi, indayace kusan kashin 40 na matsan kasar basu da aikin yi.
A cewar Adesina wanda tsohon ministan hukumar noma da raya karkara, matansa Nijeriya “sun karaya, sun fusata kasanewar suna neman makomar da bazata kai su ga gaci ba.
Wadanda Murkushe Baburan Achabar Ya Shafa
Kasancewar s ana wanda wannan lamari ya rutsa dashi, Yahaya lawal ya bayyana yadda aka kama babur dinsa.
A wata tattaunawa da PRNigeria, “ watanni 7 da suka gabata, ina kan hanya ta domin kai ziyara da mahaifina wanda tsoho, dake zaune a jihar Kano. Na dauki babur din na bawa dana domin yayi sana’ar Achaba da babur din. Amma kwanaki kadan da yin balaguron, na sami wani kira cewa jami’an karta kwana (tasksforce) sun kama babur dina, tun wancen lokacin yana tsare a hannun su.
“Maganar gaskiya, wannan babur din shine kadai abinda na mallaka. Dashi nake amfani wajen taimakawa iyaye na, na ciyar da ‘ya’yana, na kuma biya musu kudin makaranta.
“Yanzu kuma an karbe shi daga hannun mu da karfin. Ina rokon ka don girman Allah, ka taimake mu su dawo mana da babur di na.
“ku fada mususu sakar mana baburan mu, saboda idan babu shi mun gama yawo. Baza ku fahimci halin da muke ciki a yanzu ba.
“Yarana basa zuwa makaranat yanzu, an koro su gida, saboda na kasa biya musu kudin makaranta. Saboda yanzu hakan bani da aikin yi,” lawal ya fadawa PRNigeria.
Wani matukin babur din Achaba, wanda ya bayyana sunan sa da Abdulrahman, ya bukaci gwamanti ta sauya ko ta duba manufofin ta kan sana’ar ta Achaba a birnin tarayyar.
“Sana’ar Achaba itace kadai hanyar da muke bi domin mu rayu. Da ita muke amfani domin taimakawa iyalan mu. Ita kadai ce zaben daya rage mana, idan muka daina achaba zai zame mana wahala mu rayuwa cikin walwala da jin dadi.
“Gwamnati da na DRTS su daina kamawa da murkushe baburan mu. Da fatan za’a taimake mu. Mun bar Arewa maso gabas ne saboda rashin tsaro, muka dawo nan don mu samawa iyalan mu abinci.
“Amma har yanzu ba mu da ‘yancin yin kasuwanci mu na halal. Ya kamata gwamnati ta yi wani Abu, “in ji shi.
Wani magidanci dake da mata biyu, Alhaji Babangida, ya ce, “wurin da muka fito daga arewa bashi da aminci ga irin sana’ar mu. Abuja it ace kadai wurinda yawancin mu ke tunanin za mu iya yin Achaba cikin ‘yanci.
“ka tuna wasu cikin mu nada mataye 2. Wasu kuma nada hudu da tarin yara, da kuma wasu dake dogara dasu.
Babangida wanda aka kama babur dinsan babu jimawa, yace “babur din nasa yana ofishin VIO. Inda aka bukaci ya biya dubu 100 matsayin tara kafin ya karbe shi. Amma jami’an VIO ko saurare basa yi, a kokarin da nake na biyan tarar.
Martanin Kwantirolan Vio
Mista Dele YAro, mataimakin kwantrolan, sashen Sumame a shalkwatar Hukumar ta VIO a birnin tarayya Abuja, ya fadawa PRNigeria cewa gwamanti na nuna tausayi ga ‘yan Achabar dake birnin tarayyar.
“wasu kasashen dama wasu jihohi a Nijeriya sun haramta sana’ar tukin Babura. Amma nan birnin tarayya babu hana ba. Kawai mun sanya musu shinge ne da wasu wurare, a cewar sa.
Yaro yace: “Hanyoyin sufuri a babban birnin tarayya Abuja sun hadar da dogayen motoci da kanana. Daga baya muka amince da yin amfani Babura masu kafa 3 (Keke NAPEP), a unguwanni Birnin.
“akwai dalilin daya sanya mu daukar wannan mataki na takaita sana’ar Achaba anan. Mun sami rahoton lafuka da suka hadar kwacen jaka, tukin ganganci da wasu lafuka da suka shafi matuka ‘yan Achaba. Kafin mu haramta achabar a shekarar 2006, asibitocin mu sun cika makil da hadduran da ‘yan Achaban suka haddasa”.
Ya ce wayarda kan Jama’a na guda ciki nauyin daya rataya a wuyan DRTS kuma muna sauke nauyin mu.
Mataimakin kwantirolan ya kara da cewa, “ mun fara Nikawa/lalata baburan da muka kama ne bayan gudanar da zanga-zangar EndSars a shekarar 2020, inda mahaya baburan suka kutsa cikin Ofishin mu da karfin tuwo suka kuma kwashe baburan da muka kama.
“Don haka hukumar mu ta dauki gabarar lalata baburan data kama domin kiyaye aukuwar hakan nan gaba.
“Mun lalata Babura 1,500 shekarar data gabata, bayan da hukumar ta sami sahalewar babbar kotun tarayya Nijeriya.
Yaro yace sanya tara ga ‘yan Achaba dake Abuja, tamkar bayarda dama ne a cigaba da karya dokokin da aka samar.
A cewar sa “hanya daya itace a kwace babur din a lalata shi, haka ne kadai iya zama izini ga sauran.
Mun yi musu dukkannin abinda ya dace na wayar da kai. Ko da daraktan mu sai da ya zagaya birnin tarayya domin wayar musu da kai, ana tsaka da haka ya zama darakta.
“Amma duk da haka har yanzu suna karya dokokin hanya, ta yadda akasarin su ke yayo da makamai a jikin su, wanda suke amfani dasu wajen cimma al’umma. Meye yasa suke yawo da makamai indai inda abinda suke akwai gaskiya a cikin sa?
Kungiyar Matuka Babura
Shugaban kungiyar matuka baburan ta MRA dake Lugbe Yusuf Tahir, yace kungiyar na ta tsaya kai da fata wajen wayar da kan mambobin kan iyakar da aka gindaya musu, na kada su ketara zuwa manyan hanyoyi.
Haka kuma ya kara da cewa “ bama kalubalantar gwamnati kan dokar data sakawa ‘yan Achaba zuwa kwaryar birnin. Amma lalata dubunnan baburan ‘yan Achaban da aka kama ya jefa da dama cikin rishin aikin yi, wanda ke sake rura wuta rashin tsaro
“ina gani da gwamnati ta dauki gabarar horar da mambobin mu ta hanyar shirya bitoci da zasu tabbatar da su wajen dokoki da ka’idojin tuki.
“ a kuma girke jami’an tsaro dare da rana akan manya hanyoyin dake Abuja. Wannan zai taimaka wajen haramtawa ‘yan Achaban gudanar da sana’ar su a kana titunan.
“ ina tunani lalata baburan da da aka kama na kara ta’azza gudanar da muggana laifuka. Haka kuma wasu baburan ma’aikatan gwamnati ne suka sayawa matukan domin sake samun kudin shi.
“idan aka lalata baburan da aka kama hakan ka iya zama gagarumar matsala ga mai dukiyar da kuma wanda ke sarrafa ta. Don haka za’a iya saka tara ga wanda ya karya doka. Ko kuma VIO suja hankali ma’aikatan gwamnati dasu san suwa suke bawa dukiyar s uku kuma su basu shawarar bayar da baburan ga matasan da suka san yakamata.

Mafita daga kwararru
Sanata Iruegbi, wani mai sharhi kan abinda ya shafi Al’umma, ya nuna bacin rai kan matakin da Gwamnatin ta dauak na lalata baburan daga kama, yace: “ ina ganin wannan lamari ne da za’a kira matsayin “Catch-22”, wanda ko dai ya kamata ku mayar da hankali kan tsaron sama da tsaftace muhalli da kyawun birni. Ko kuma akasin haka. Amma kamawa da lalata Babura Achaba ka iya haifar da sakamako maras kyau.
Iruegbo, wanda babban Adita ne a Global Sentinel, ya yi Karin haske game da zamantake hadi da tsaro kan dokar Achaba a cikin birnin Abuja.
Ya ce; “ka ga an yi asara mai tarin yawa domin wadanda abin ya shafa ba kawai baburansu ba ne kawai suka rasa, sun rasa kkudin da sukayi amfani dashi wajen sayo su, da kuma abin suke dogaro da shi.
“duk da haka, kamar yadda na ambata a baya har yanzu gwamnati na bukatar ta kula da tsarin da kuma samar da nutsuwa a cikin babban birnin tarayya Abuja, da kuma gujewa gurbacewar muhalli sanadiyyar ‘yan Achaba.
“ fiye da wannan, ya kamata a samar da mafitar da zata sanya kowa ya gamsu. Ma’ana, ya kamata matuka baburan su rike sana’ar sub a tare da kawo tasgaro ga tsaron da muhalli ga birnin tarayyar kasar ba.
Shima a nasa bangare Mista Chidi Omeje, kwararre a harkar tsaro a Abuja, yayi wwatsi da manufar murkushe ‘yan Achaba.
Yace: “Al’amarin yayi muni sosai. Hakan ya nuna irin zaluncin da gwamanti da hukumominta ke yin a lalata hanyoyin rayuwa da wasu ‘yan Nijeriya amfani da ita.
“ta hanyar Murkushe mashinan Achaba na mutane, kuna kuna kiwon masu aikata laifuka; mutanen da basu da wani abu da zasu ji fargabar rasawa, zasu saki tudun dafarwar su, su kuma yada ta’addanci a cikin Al’umma.
An samar da wannan rahoto ne bisa tallafin cibiyar Nazarin Harkokin Jarida ta wole Soyinka (WSCIJ) a karkashin Hadin Gwiwar Media Engagement for development inclusivity da Accountability Project (CMEDIA) wanda gidauniyar MacArthur ta samar.
By PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 23 hours 36 minutes 47 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 1 hour 18 minutes 12 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com