Gwamnatin Jihar Kano a Arewacin Najeriya ta ce nan da makwanni 6 za a kammala aikin tashar samar da wutar lantarki ta Tiga mai karfin mega watt 10
Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya ba da tabbacin ne lokacin ziyarar ganin yadda aikin tashar samar da wutar lantarki na Tiga da na samar da ruwa da ke Tamburawa yake gudana.
Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Malam Abba Anwar ya fitar a jihar Kano, ta ce tashar samar da wutar lantarkin a matakin gwaji kafin kaddamarwa.
Gwamnan ya kuma yabawa kamfanin samar da hasken wutar lantarki mallakin jihar KHEDCO da kamfanin da aka baiwa kwangilar aiki da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
A cewar gwamnan na da makwanni kadan wutar lantarkin na Tiga za a jona shi da tashar samar da ruwa ta Tamburawa , yana mai bada tabbacin cewa zai yi iyakar kokari dan ganin ya bar tarihi a dukkanin bangarorin ciyar da al’umma gaba.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 1 minute 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 43 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com