Wani jirgin soji mai saukar angulu kirar Mi-17, ya yi hadadi a filin sauka da tashin jiragen saman birnin Yamai da ke jamhuriyar Nijar, inda mutane uku da ke cikinsa suka rasa rayukansu nan take.
Ma’aikatar tsaron kasar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 da mintuna 40 na safe.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wata sanarwa da ma’aikatar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar a tsakiyar ranar litinin, ta ce jirgin ya yi hadari ne lokacin da yake sauka, bayan dawowa daga atisayen bayar da horo, kuma wadanda suka rasa rayukansu sun hadar da babban hafsan soji daya, da karamin hafsa daya sai kuma wanda ke horas da su dan asalin wata kasa ta kerare.
Ma’aikatar tsaron ta ce tuni ta kaddamar da bincike domin gano musababbin wannan hadari, tare da bayyana juyayi dangane da faruwar lamarin.
PRNigeria hausa












