Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta kama wasu da ake zargi da aikata daba ta hanyar amfani da wuƙaƙe suna gallaza wa mutane a birnin Kano.
A cewar bayanai daga wajen waɗanda ayyukan ƴan dabar ya shafa, sun ce mutanen da ake tuhuma kan yi amfani da tituna masu cunkoso da wuraren taron jama’a don aikata ta’asar.
Duk da matsalar rashin tsaro, Kano cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya, ta kasance cikin kwanciyar hankali har sai da aka samu gungun masu riƙe da wuƙaƙe.
Read Also:
Ayyukan ƴan dabar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bayan far musu da ɓata garin suka yi, yayin da waɗanda suka samu tsira kuma ke gamuwa da munanan raunuka.
’Yan dabar – waɗanda rundunar ‘yan sandan ta Anti-Daba ta kama – sun yi ƙaurin suna wajen amfani da wurare masu cunkoso don cin zarafin jama’a da rana tsaka.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi kira ga jama’a da su taimaka rundunar wajen gano sauran ‘yan ƙungiyar dake cikin ƙwaryar birnin.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 20 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 1 minute 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com