Gwamnatin Najeriya ta ce sabon tsarin mafi karancin albashi zai fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Afrilun 2024.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na kasar, Idris Mohammed, wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja, ya ce tsarin mafi ƙarancin albashi na naira 30,000 na yanzu zai daina aiki ne a karshen watan Maris na shekarar 2024.
Mohammed ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin nazarin kasafin kudi na shekarar 2024-2026 da shugaba Tinubu ya gabatar inda ya ce za a kashe naira tiriliyan 24.66 kan albashi a shekarar 2024 da 2025 da kuma 2026.
Bayan cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, gwamnatin tarayya ta amince ta bai wa kowane ma’aikacinta tallafin naira 35,000 domin rage raɗaɗin cire tallafin.
Read Also:
Sai dai kungiyar ƙwadago ta dage kan cewa tallafin naira 35,000 na wucin-gadi bai wadatar ba, inda ta kara da cewa ya kamata a sake duba mafi karancin albashi a shekarar 2024.
Tawagar Gwamnatin Tarayya da Majalisar Tattaunawar Ma’aikata ta Kasa a ranar 18 ga Oktoba, 2019, sun amince da aiwatar da mafi karancin albashi na naira 30,00 bayan shafe watanni ana tattaunawa.
Sai dai a ranar Alhamis kungiyar kwadago ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da gwamnatin tarayya, inda ta kara da cewa bisa tsarin dokar kwadagon kasar ya kamata a sake duba mafi karancin albashi duk bayan shekaru biyar.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero, ya ce kwanan nan, “Sake duba mafi ƙarancin albashi na kasa lamari ne na doka da ake sa ran zai faru a 2024.”
A nasa ɓangaren, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed, ya shaida cewa, ƙarin albashin na da nufin maye gurbin matakin wucin-gadi da gwamnati ta sanya don magance wahalhalun da ke tattare da cire tallafin man fetur.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 6 hours 44 minutes 13 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 8 hours 25 minutes 38 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com