Gwamnatin jihar kaduna ta dora alhakin harin daya hallaka mutane sama da 30 a jihar Kaduna kan dakarun sojojin saman Nijeriya.
ta cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fita ta bayyana cewa gwamantin jihar ta sami wani bayanin tsaro a daren ranar lahadi dake cewa wani harin sama kan fararen hula yayi sanadiyyar mutuwar mutane masu tarin yawa a jihar dake arewa maso yammacin kasar.
a yayin wani taron majalisar tsaro bisa jagorancin mataimakiyar gwamnan Jihar Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, wanda ya sami halartar shuwagannin tsaro da na gargajiya, rundunar sojojin Nijeriya ta yi bayani kan lamarin wanda ya haifar da harin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Jagoran dake lura da shiyya ta daya ta dakarun sojin Manjo VU Okoro ya yi bayyana cewa dakarun sojojin na zagayen ganin sun kawar da ‘yan ta’adda amma cikin kuskure harin ya hau kan Al’ummar dake cikin garin.
mataimakiyar gwamnan a yayin rufe taron ta miki ta’aziiyar gwamnatin jihar ga Al’ummar jihar kaduna da ‘yan uwa da iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da neman gafara ga wadanda lamarin ya auku a kan su.
taron dai ya samu halartar kwamshinan ‘yan sandan jihar My Garba, daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) Abdul Eneche, shugaban kungiyar JNI na jihar Kaduna Farfesa Shafi’u Abdullahi, wanda ya jagoranci shuwagabannin addinai, haka kuma akwai dagacin Rigasa Alhaji Aminu Idris wanda a yankin sa harin ya faru.












