Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga al’ummar Namibiya bisa rasuwar shugaban ƙasar Hage Geingob.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce ya kaɗu da jin labarin rasuwar mista Geingob, wanda ya bayyana da ɗan kishin gwagwarmayar tabbatar da dimokraɗiyya.
Read Also:
Shugaban na Najeriya ya kuma bayyana marigayin da jagoran tabbatar da jagoranci nagari, da bunƙasa tattalin arziki da ci gaba al’ummar Afirka.
Shugaba Tinubu ya ce marigayin ya rasu ne a daidai lokacin da nahiyar Afirka ke buƙatar jajirtattun shugabanni irinsa, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen bunƙasa nahiyar ta ko wanne fannin ci gaba.
Daga ƙarshe shugaba Tinubu ya ce a madadin gwamnatinsa da al’ummar Najeriya suna miƙa saƙon ta’aziyyarsu ga ɗaukacin al’ummar Nambiya bisa wannan babban rashi da suka yi.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 20 hours 12 minutes 19 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 53 minutes 44 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com