‘Yan bindiga sun fara neman sulhu a Nijeriya

Tun bayan da gwamnatin Nijeriya ta haramta biyan kudin fansa, tare da barin wuta da sojojin kasar ke yi kan ‘yan bindigar daji, guda cikin shuwagabannin kungiyoyin ‘yan ta’addan dajin masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ya nemi sulhu.

Wannan dai na zuwa ne tun bayan da mai bawa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa gwamantin tarayya ta haramta biyan kudin fansa domin kubutar da wadanda da masu garkuwa da mutane suka kama.

Shugaban ‘yan ta’addan da ya kira kansa Gabar Haliyu, da yake Magana da turancin Pigin inda yake jawabi ga mambobin dabar sa.

Ta cikin wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu, haliyu na bayyana cewa biyan fansar wajibi ne domin tseratar da rayuka, da kuma barin Gwamnan jihar zamfara Dauda Lawan Dare ya gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali.

Haka dai PRNigeria ta tattara cewa manyan masu fada a ji a cikin Fulani da aka fi sani da Ardo sun bukaci ‘yan ta’addan da su aje makamansu domin samun zaman lafiya mai dorewa.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 33 minutes 2 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 14 minutes 27 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com