Rundunar dakarun ƙasashen da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram ta MNJTF ta ce ƙarin ƴan ta’adda shida sun sake miƙa wuya tare da ajiye makamansu.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar, leftena kanar, Abubakar Abdullahi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A cewar sanarwar, wani ɗan Boko Haram mai shekara 19 ya miƙa wuya ga sojojin runduna ta 403 da ke Monguno.
Binciken farko, a cewar sanarwar ta nuna cewa matashin na da alaƙa ta kusan shekara uku da ɓangaren Buduma na Boko Haram.
Read Also:
Ƙarin mayaƙa biyu – ɗan shekara 37 da 21 sun miƙa kansu a Blangua da ke Kamaru ga dakarun runduna ta ɗaya da ke yankin Darak a kudancin tafkin Chadi. Binciken da aka yi a kansu ya nuna ƴan asalin Chadi ne da ke zama a yankunan Kami-Wari da Kourea.
Sai kuma wani ɗan shekara 38 da mai ɗakinsa da ƴaƴansu biyu – ɗan shekara 13 da jaririya sun kai kansu ga sojojin runduna ta uku a yankin Baga da ke Najeriya.
Haka nan, sanarwar ta ce wani ɗan shekara 25 shi ma ya miƙa kansa ga sojojin runduna ta uku a Kekeno da ke ƙarmar hukumar Kukawa a jihar Borno inda ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun yi garkuwa da shi a kan titin Monguno zuwa Maiduguri a shekarar 2020.
Ya bayyana cewa a lokacin da aka kama shi, an tilasta masa yin aiki a matsayin mai gadi a ɗaya daga cikin sansanonin ƙungiyar da ke tafkin chadi.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 23 hours 26 minutes 13 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 1 hour 7 minutes 38 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com