Ba mu muka kama matashin da ya buga rigunan zanga-zanga a Kano ba – DSS

Ba mu muka kama matashin da ya buga rigunan zanga-zanga a Kano ba – DSS

Hukumar tsaro ta DSS ta musanta labarin da ke cewa jami’anta sun kama wani matashi a jihar Kano da ke sayar da riguna domin shirin gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Nijeriya ta ‘#EndBadGovernanceInNigeria’.

Tun da fari dai tsohon ɗan takarar Shugaban Kasa karkashin inuwar jam’iyyar AAC a zaben 2023, Omoyele Sowore ne ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin cewa jami’an DSS din sun kama matashin dan asalin jihar Kano mai suna Bashir Abubakar.

Sowere ya ce DSS a ranar Litinin sun saki guda cikin wadanda suke shirya zanga-zangar ta da za a yi a watan Agusta.

Ya rubuta, “tawagar lauyoyin da aka turawa @OfficialDSSNG sun sami nasarar kubutar da Bashir Abubakar daga hannun jami’an na DSS.

“Bashir matashin dan gwagwarmaya ne daga Kano, wanda ake zargi da samar da riguna masu dauke da rubutun #EndBadGovernanceInNigeria a jihar Kano.”

Sai dai ko da aka tambayi Kakakin hukumar na kasa, Peter Ifunanya kai tsaye ya kada baki ya ce, “ba gaskiya ba ne,” kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Idan za a iya tunawa ko bayan zanga-zangar kin jinin jami’an tsaro ta #EndARs a Nijeriya, wasu bayanani da jaridar PRNigeria ta tattara wanda ta yi wa lakabi da “101 Fake news on EndSars protest” sun nuna irin tarin karairayin da aka yi amfani da su wajen assasa zanga-zangar wadda ta bar baya da kura a kasar.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 29 minutes 23 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 10 minutes 48 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com