Jagoran jam’iyyar NNPP a kasar nan, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi kira ga ‘yan ƙasar da ke shirin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da su yi amfani da ƙuri’arsu wajen sauya shugabannin, maimaikon fitowa zanga-zangar.
Kwankwaso ya ce ƙasar ta tsinci kanta a halin matsin rayuwa da take ciki ne sakamakon kasa ɗaukar matakan da suka dace da jagororin ƙasar suka yi tun a shekarar 2007.
Cikin wata sanarwa da jagoran Kwankwansiyyar ya fitar ya ce har yanzu lokaci bai ƙure ba, na yadda za a farfaɗo da ƙasar da samar wa al’umma abubuwan ci-gaba da na walwala.
Ya ci gaba da cewa hakan zai yiwu ne kawai ta hanyar samar da shugabanci nagari, da bin doka da kyakkyawan tsari dayin abubuwa yadda suka dace.
Inda yace abin takaici ne yadda halayen shugabanninmu na rashin iya mulki suka jefa ƙasar nan musamman matasa cikin yunwa da rashin tsaro da fusata ta yadda har wasu daga cikinsu suka fara yanke ƙauna game da gyaruwar ƙasar,
Wasu matasan Najeriyar na shirin gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna damuwarsu kan halin matsi da tsadar rayuwa da sauran matsalolin da al’ummar ƙasar ke fuskanta.
To sai dai Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya da hannu a haifar da wasu matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Read Also:
”Sa bakin gwamnatin tarayya a batun sarautar Kano, da tsige mataimakin gwamnan Edo da rikicin siyasar jihar Rivers da yi wa matatar mai ta Dangote zagon-ƙasa, da ce-ce-ce-ku-cen da yarjejeniyar SAMOA ta haifar, da rikici tsakanin Sanata Ali Ndume da APC, da rashin tsaro da sauran miyagun laifukan da za a iya kauce musu na daga cikin misalan abubuwan da suka haifar da matsalolin da ake fuskanta a ƙasar nan”, in ji Kwankwaso.
Jagoran NNPP ya ce duk da cewa zanga-zangar adawa da tsadar rayuwar, hanya ce da matasan za su nuna wa shugabbanni damuwarsu, amma ya ce yana da kyau matasan da ke shirin gudanar da zanga-zangar su sanya muradun ƙasar a gaba fiye da komai.
Ya kira ga matasan ƙasar su zama masu haƙuri da gwamnatin, ta hanyar ba ta duk wata dama da goyon baya domin ta cimma nasara.
”A ƙarshe duk shugabannin da suka gaza, muna da dama a matsayinmu na ‘yan ƙasa mu yi amfani da ƙuri’unmu, don zaɓar wasu da muke ganin za su kawo mana ci gaban da muke buƙata”, in ji shi.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 45 minutes 20 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 26 minutes 45 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com