Rundunar sojin Nijeriya tace zata saka hannun muddin tashe tashen hankula suka cigaba da aukuwa a wasu jihohin kasar nan sakamakon zanga – zangar yaki da talauci da tsadar rayuwa.
Shugaban dakarun soji Janar Christopphare Musa ne yabbayan hakan, yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, inda yace dakarun sojoji zasu fita domin magance wasu tashe tashen hankula ta baranatar da dukiya dake faru a wasu sassan kasar nan.
Read Also:
Rahotannin sun bayyana cewa sakamakon zangar zangar ya haifar da mutuwar akalla mutane 17 a birnin Abuja, kano niger, Borno, Kaduna da kuma Jihar jigawa, inda aka balle bankuna wuraren kasuwanci, yayin da hanyoyi da dama aka lalata su.
A wasu sassan kasar nan zanga-zangar ta cigaba bayan da aka yi arangama tsakanin dakarun ‘yan sanda da masu zanga-zangar a fadin kasar nan.
Christopher yace suna sane da yunkurin Al’umma na yin zanga-zanga domin nuna bacin ransu kan tsadar rayuwar da suke ciki a fadin Nijeriya.
Daga bisani ya bukaci Al’ummar Nijeriya dasu hada kai, wajen kawar da kai da kuma haramtawa kan su daukar kayan mutane a yayin da kuma bayan zanga-zangar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 20 minutes 16 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 1 minute 41 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com