Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa zai mutunta gayyatar da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi masa a ranar Laraba 29 ga watan Agustan 2024, maimakon yau Talata 20 ga watan Agustan 2024 kamar yadda aka buƙata tun farko.
A cikin wata wasiƙa da shugaban ƙwadagon ya aika wa ƴansanda ta hannun lauyoyinsa, Ajaero ya bayyana cewa, wasikar gayyatar ta same shi ne a jiya Litinin, kuma shugaban yana da wasu ayyukan da ya tsara gudanarwa a yau Talata.
Sai dai sanarwar ta ce Ajaero a shirye yake ya amsa gayyatar a ranar Laraba.
Bugu da kari, Ajaero ya buƙaci ƴansanda da su bayar da cikakkun bayanai game da zargin da ake yi masa, waɗanda suka haɗa da samar da kuɗaɗen tallafa wa ayyukan ta’addanci da haɗa baki wajen aikata laifuffuka da cin amanar ƙasa, da kuma aikata laifuka ta shafukan intanet.
Wasiƙar ta ambato sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa wanda ake tuhuma ƴancin samun cikakken bayani game da yanayi da takamaiman zarge-zargen da ake yi masa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 59 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 40 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com