Nijeriya ta karbi kashin farko na Allurar rigakafin Kyandar biri da Amurka

Sunƙin farko ɗauke da allurar rigakafin cutar ƙyandar biri guda dubu 10 ya isa Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Talata.

Amurka ce dai ta bayar da tallafin allurar rigakafin da kamfanin ƙasar Denmark, Bavarian Nordic ya samar da manufar daƙile nau’in cutar ƙyandar birin ta Clade II, wadda ƙwayar cuta ce da ba ta illa sosai wadda kuma ita ce take yaɗuwa a ƙasar tun shekarar 2017, kamar yadda BBC ta rawaito.

Najeriya dai ta samu mutum fiye da 700 da ake zargin sun kamu da cutar ta kyandar biri inda aka tabbatar da kamuwar mutum 40, duk da cewa ƙwayar cutar da ta kama dukkanninsu ba mai zafi ba ce.

Cutar ta yaɗu zuwa jihohi 13 a Najeriya da suka haɗa da jihohin Bayelsa da Cross River da Ogun da Legas inda nan ne cutar ta fi shafa.

Najeriya ta ce za ta bai wa jami’an lafiya da garuruwan da ke fuskantar haɗarin kamuwa da cutar fifiko wajen allurar rigakafin.

Cibiyar da ke daƙile cutuka masu yaɗuwa a Afirka ta CDD ta yi ƙiyasin cewa ana buƙatar allurar guda miliyan 10 a nahiyar.

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ce ƙasar da nau’in cutar mai zafi na Clade 1b ya fi yi wa illa a nahiyar.

Tun dai watan Janairun 2023 ne jamhuriyar ta Dimokraɗiyar Congo ta ayyana ɓullar cutar inda mutum dubu 27 suka kamu sannan fiye da 1000 suka mutu.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 13 hours 37 minutes 30 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 15 hours 18 minutes 55 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com