Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki dake lura da shiyyar Kano, jigawa da katsina KEDCO ta nemi afuwar abokan huldarta bisa karancin wutar da aka samu a ‘yan tsakanin nan.
kamfanin ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban dake lura da sashen raba wutar lantarki na shiyyar, Engr. Kasim Abdullahi Burkullo a yayin da yake ganawa da manema labarai a shalkwatar hukumar dake jihar Kano.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci kwamitinta da ke kula da harkokin wutar lantarki ya gudanar da bincike kan matsalar yawan lalacewar layin samar da lantarki na ƙasar, ya kuma bayar da rahoto cikin mako uku.
Matakin ya biyo bayan amincewa da buƙatar da ɗan majalisar Mansur Mano Soro, daga jihar Bauchi ya gabatar a zamanta na yau Laraba.
Ɗan majalisar ya bayyana damuwa kan matsalar lalacewar layin lantarkin na ƙasa da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a kwanakin nan, lamarin da ke jefa ƙasar cikin rashin wuta tare da jefa ‘yan ƙasar cikin matsin rayuwa da suke fama da shi.
Ya ce, wutar lantarki aba ce da ta zama wajibi wajen bunƙasar tattalin arziƙi da kuma cigaban duk wata ƙasa.
Hon. Mansur ya nuna takaicinsa yadda aka samu matsalar lalacewar layin wutar na ƙasa sau takwas a cikin wannan shekara ta 2024 kaɗai, inda ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa da takaici.
Ɗan majalisar ya ce sakamakon matsalar lalacewar, gaba ɗaya yankin arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas na ƙasar sun kasance cikin duhu, da uwa uba ƙarin tsanani na tsadar rayuwa.
Ya ƙara da cewa abin takaici ne yadda matsalar ke faruwa a daidai lokacin da ministan wutar lantarkin ke ba wa ‘yan Najeriya tabbacin ingancin samar da wutar, abin da ya sa har gwamnati ta ce ya sa dole ta ƙara kuɗin wutar ga masu amfani da ita na rukunin farko ko babban layi (Band A).
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 22 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 3 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com