Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 25 ne suka ci gajiyar shirin raba kuɗin tallafi na ₦25,000 zuwa yanzu, abin da ke temakawa matuƙa yayin da ake aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.
Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Alhamis.
Bayanin ya biyo bayan taron Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa (NEC), wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranta a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.
Da yake bayyana matakan da gwamnatin ke ɗauka domin rage wa ƴan Najeriya nauyin tattalin arziƙi a sakamakon cire tallafin man fetur da sauran tsare-tsaren sauye-sauyen kuɗaɗe, Mista Edun ya yi nuni da ƙoƙarin rage wa mutane ƙunci da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi.
“Ana hasashen cewa gidaje miliyan biyar ne suka ci gajiyar shirin raba kuɗi kai-tsaye,” in ji shi, yana mai jaddada yawan waɗanda suka amfana da shirin.
Bugu da ƙari, Mista Edun ya bayyana cewa kimanin mutane 11,000 ne suka karɓi naira biliyan 3.5 a ƙarƙashin tsarin ba da rance na kayan amfani a cikin kwanaki biyar da suka gabata.
Haka kuma, ya sanar da cewa fiye da naira biliyan 90 sun samu shiga cikin shirin ba da rancen ɗalibai, wanda ke taimaka wa ɗalibai kusan rabin miliyan na Najeriya wajen cimma burin iliminsu.
Read Also:
Taron NEC ɗin ya kuma tattauna batun matsalar ambaliyar ruwa da ta addabi al’umma a faɗin Najeriya.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima, tare da Majalisar, sun bayyana damuwa matuƙa kan asarar rayuka da kuma asarar dukiyoyi da aka samu.
Ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla ƴan Najeriya 321 a faɗin jihohi 34, inda fiye da mutane miliyan 1.2 suka rasa muhallansu kuma fiye da gidaje miliyan ɗaya suka lalace.
Bayan taron, Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya yi jawabi ga manema labarai, inda ya bayyana yadda ambaliyar ta shafi rayuwar jama’a da kuma harkar noma.
“Ana samun asara sosai a gonaki, inda ambaliyar ta wanke gonaki, ta bar dubban ƴan Najeriya ba tare da gidaje ko hanyoyin samun abinci ba,” in ji shi.
Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa ta bukaci ɗaukar matakin gaggawa don rage wahalhalun da waɗanda ambaliyar ta shafa ke fuskanta, sannan ta roƙi hukumomin gwamnati su ƙara ƙoƙari wajen samar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.
Waɗannan matakan na nuna sadaukarwar gwamnati wajen tallafa wa ƴan Najeriya a lokacin wahala, ko ta hanyar ba da tallafin kuɗi ko kuma ɗaukar matakin gaggawa domin tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa, duba da irin ƙalubalen tattalin arziki da na muhalli da ake fuskanta a wannan lokaci.
To sai dai kuma, abin tambayar shine, ko tsare-tsaren na tasiri? Abin da za a jira a gani kenan.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 3 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 44 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com