Muna so majalisa ta gaggauta amincewa da sabbin dokokinmu – INEC

Shugaban hukumar zaɓe ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya buƙaci majalisar dokokin Najeriya da ta gaggauta amincewa da sabbin sauye-sauyen dokokin zaɓe na ƙasar.

Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Abuja yayin wata ganawa da tawagar sa ido kan zaɓe ta Tarayyar Turai (EU) ƙarƙashin jagorancin Barry Andrews, wanda shi ma ya jagoranci sa ido a babban zaɓen 2023.

A farkon shekarar nan ne dai hukumar INEC ta aikewa majalisa wasu dokoki da take so a yi gyara da suka haɗa da:

  • Zaɓen wuri (Early Voting)
  • Zaɓen mazauna ƙasashen waje (Diaspora Voting)
  • Gyara amfani da katin zaɓe na dindindin
  • Bai wa INEC damar naɗa shugabannin zaɓe na jihohi
  • Samar da hukumomin sasanta rikicin zaɓe

Farfesa Yakubu ya jaddada cewa amincewa da sabbin dokokin da wuri zai taimaka wa INEC wajen tsara shirye-shirye cikin nasara kafin babban zaɓe na gaba.

Ya bayyana cewa hukumar INEC ta yi nazari sosai kan dukkan shawarwari guda takwas da masu sa ido kan zaɓe ta EU ta bayar da suka shafi hukumar kai tsaye a rahotonsu na zaɓen 2023.

Yakubu ya ce hukumar ta riga ta ɗauki matakai a kan waɗanda ke buƙatar sauye-sauye cikin gida, sannan tana aiki tare da sauran sassa kan shawarwari da suka shafi kowa.

Ya kuma ce hukumar tana jiran kammala nazarin sauye-sauyen doka da majalisar dokoki ke yi.

Shugaban INEC ɗin ya ƙara da cewa shawarwarin EU da na sauran masu sa ido, na cikin muhimman abubuwan da aka yi la’akari da su yayin nazarin bayan zaɓe na 2023.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com