Likitoci masu neman ƙwarewa na yajin aiki a Najeriya

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa Najeriya (NARD) sun fara yajin aiki na dindindin daga ranar Asabar, lamarin da ya tsayar da ayyuka da dama a cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin ƙasar.

Shugaban NARD, Dakta Mohammad Suleiman, ya tabbatar da fara yajin aikin a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar.

Wannan yajin aiki na zuwa ne bayan cikar wa’adin kwanaki 30 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya kan ta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka yi a baya.

Dakta Suleiman ya ce yajin aikin ya zama dole ne bayan gwamantin ta kasa aiwatar da yarjejeniyar da ake da ita duk da tarurruka da roƙe-roƙe da gargaɗi da ƙungiyar ta yi.

“Buƙatunmu ba wai na son kai ne ko siyasa ba, muna neman yanayi mai kyau da zai bai wa likitoci damar yin aiki cikin aminci da kulawa da inganci ga marasa lafiya ba tare da hatsarin lafiyar su ba,” in ji shi.

Daga cikin manyan ƙorafe-ƙorafen NARD sun haɗa da albashin da ba a biyasu ba da rashin kyawawan yanayin aiki da ƙarancin ma’aikata, nauyin aiki mai yawa, da kuma rashin kayan aiki na asibiti, waɗanda ya ce sun lalata tsarin kiwon lafiya a faɗin ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com