Kotu da dakatar da ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa daga shiga yajin aiki

Kotun ƙwadago a Najeriya ta dakatar da shirin ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasar na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani da suka tsara farawa daga ranar 12 ga watan da muke na Janairun.

Kotun ƙwadagon ta Najeriyar ƙarƙashin mai shari’a Justice Emmanuel Subilim a jiya Juma’a ta umarci shugaban ƙungiyar ta NARD Dr Mohammad Usman Suleiman da sakataren ƙungiyar Dr Shu’aibu Ibrahim da su dakatar da aniyar tsunduma yajin aikin.

Tun farko gwamnatin Najeriya ƙarƙashin ofishin ministan shari’a ne ta garzaya kotun don dakatar da likitocin daga faro wannan yajin aiki da ta ce zai kassara harkokin kulawar lafiya.

Cikin takardar da ke ɗauke da umarnin kotun, Mai shari’a Subilim ya haramtawa ƙungiyar duk wani shirin bore ko ƙauracewa aiki ta kowacce fuska, har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren shari’ar a ranar 21 ga watan nan.

Kafin wannan hukunci tarin asibitoci a sassan Najeriya ciki har da na koyarwa sun fara amsa kiran uwar ƙungiyar ta NARD wajen faro yajin aikin a ranar Litinin mai zuwa.

Sanarwar NARD da tun farko ta buƙaci tafiya yajin aikin ɗauke da sa hannun shugabanta Dr Suleiman ta ce an cimma matsayar tsunduma yajin aiki na sai baba ta gani ne yayin babban taron ƙungiyar na ranar 2 ga watan nan sakamakon gaza samun daidaito tsakaninsu da gwamnatin Najeriya kan jerin buƙatunsu na haƙƙoki da aka gaza biyansu dama alƙawuran da gwamnatin ƙasar ta gaza cika musu.

Wannan yajin aiki da suka yiwa ta ke da “Ba aiwatarwa ba komawa bakin aiki” ana ganin zai kasance mafi tsanani da ƙungiyar ta taɓa idan har da ta yi nasarar faro shi ganin cewa likitocin ba za su koma bakin aiki ba har sai an aiwatar da dukkanin buƙatunsu.

Tsawon lokaci aka shafe ana kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Najeriya da ƙungiyoyin ma’aikatan ɓangaren lafiya kama daga Likitocin da takwarorinsu malaman jinya lamarin da kan kai ga yajin aiki a lokuta dama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com