Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi yadda yace ana matsa wa wasu shugabannin ƙananan hukumomi lamba domin su fice daga tsarin Kwankwasiyya.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yau Talata, cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Read Also:
In da ya ce ya samu kiraye-kiraye daga wasu shugabannin ƙananan hukumomi da kuma ’yan Majalisar Jiha, inda ake buƙatar su sanya hannu domin komawa jam’iyyar APC.
Ya ƙara da cewa yana ƙarfafa gwiwar masu ci gaba da kasancewa cikin tsarin Kwankwasiyya, tare da ba su tabbacin cewa za su yi aiki tare domin fuskantar zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
Daga bisani Kwankwaso ya yabawa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya yabi Gwamnatinsa ya kuma kushe gwamnatin da ta gabata.










