Gwamnatin jihar Kano ta fitar da wata sanarwa domin yin ƙarin haske kan ganawar da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi da shugaban Najeriya Bola Tinubu.
A yammacin Litinin ne gwamnan, wanda aka daɗe ana raɗe-raɗin komawarsa jam’iyyar APC mai mulki daga jam’iyyar NNPP ya gana da Bola Tinubu, inda ake sa ran cewa tattaunawar ta ƙunshi batun cimma yarjejeniya kan sauya sheƙar gwamnan.
Sai dai a sanarwar da gwamnatin ta fitar ta hannun mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, ta ce gwamnan da shugaban ƙasa sun tattauna ne kan muhimman abubuwa da suka shafi tsaro da samar da ayyukan more rayuwa.
Sanarwar ta ce ganawar, wadda aka yi a asirce, “ta bai wa gwamnan damar yi wa shugaban ƙasa bayani kan manyan ƙalubale da jihar Kano ke fuskanta musamman taɓarɓarewar tsaro a wasu ƙananan hukumomi.
“Gwamna Yusuf ya kuma yi wa shugaban ƙarin bayani kan matar da aka kashe da ’ya’yanta shida kwanan nan, yana mai jaddada buƙatar gaggawar tallafin gwamnatin tarayya domin ƙarfafa ayyukan tsaro da kare rayukan fararen hula.
“Ya kuma bayyana rawar da Rundunar Tsaro ta Jihar Kano ke takawa wajen taimaka wa hukumomin tsaro, tare da neman ƙarin haɗin gwiwa da hukumomin tsaron tarayya.
“A ɓangaren raya ƙasa, gwamnan ya tattauna manufar ci gaban Kano, inda ya mayar da hankali kan manyan ayyukan gine-gine.
“A nasa ɓangaren, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa gwamnan cewa “gwamnatin tarayya a shirye take ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Kano domin shawo kan matsalolin tsaro da kuma tabbatar da ci gaba mai ɗorewa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.











