A jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya, rahotanni sun nuna cewa wasu ƴanbindiga sun yi garkuwa da sama da mutane 160 a wasu coci-coci da ke ƙauyen Kurmin Wali a ƙaramar hukumar Kajuru a jihar. Lamarin dai ya auku ne ranar Lahadi, lokacin da mutanen ke ibada a coci da ke ƙauyen.
Shi ma shugaban ƙungiyar kiristoci ta Najeriya CAN, reshen jihar Kaduna Reberan Joseph John Hayab ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce, “duk da cewa ban cika son ambata adadi ba, amma bayanan da na samu daga yankin na nuna cewa ƴanbindiga sun sace kusan mutum 172, amma guda 9 sun tsere sun koma gida, amma har yanzu ana neman mutum 163,” in ji shi.
Ya ce ko ma dai mene ne maƙasudin sace mutanen, “ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba. Za mu ci gaba da ba jami’an tsaro da gwamnati haɗin kai domin tabbatar da ceto mutanen.”
Har zuwa lokacin haɗa wannan labarin dai gwamnatin jihar Kaduna da rundunar ƴansandan jihar ba su ce komai ba.












