Mayakan Boko Haram sun kutsa cikin ayarin sojin Najariya da bama-bamai a Borno

Wani ɗan ƙunar baƙin wake ya afkawa ayarin motocin sojoji a yankin Timbuktu da ke jihar Borno, inda ya kashe sojoji biyar tare da raunata wasu da dama da ba a fayyace adadinsu ba, majiyoyin tsaro sun tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa manyan jami’an soja biyu – Manjo da Laftanar  na daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su.

Majiyar soji ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa, sojojin na dawowa ne daga wani aikin kakkabe ƴan ta’adda a filin daga, wanda ya yi nasarar tarwatsa sansanonin Boko Haram da dama tare da kashe da yawa daga cikinsu.

sojojin na kan hanyarsu na dawo daga samamen da suka kaddamar domin kakkabe mayakan Boko Haram a yankin, inda dakarun sojin suka samu nasara sosai.

Ɗaya daga cikin sojojin ya ce, harin ya yi ɓarna sosai tare da lalata kayan aikin da sojojin suka yi amfani da su yayin aikin sharar dajin na tsawon makonni.

Ya ce ƴan ta’addan sun yi amfani da wata mota makare da abubuwa masu fashewa wajen kutsawa cikin ayarin motocin sojoji dake tafiya a kan hanya.

Ya ce motocin sulke da na jigilar kaya sun lalace lokacin da motar da ke ɗauke da abubuwan fashewa ta afka wa ayarin motocin ranar Talata.

Rahotanni, an kai gawarwakin sojojin da suka mutu zuwa Maiduguri babban birin jihar Borno, yayin da aka kuma kai jami’an da suka ji rauni a harin zuwa wani asibiti don kulawar da lafiyarsu.

A wannan wuri da ake kira Timbuktu nan ne ƴan ta’adda suka yi wa tawagar Brigadier Janar Musa Uba kwanton ɓauna, suka kama shi tare da yi masa kisan gilla.

A ranar Litinin, Sojoji ƙarƙashin rundunar haɗin guiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI suka sanar da samu nasarori wajen kakkaɓe sansanonin ƴan ta’adda da dama tare da dakile hare-haren jiragen sama marasa matuki a yankin.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar, ta ce sun kuma ƙwato makamai da kayan aiki daga hannun ƴan ta’addan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com