Amurka da Najeriya sun yi taron farko a Abuja domin ƙarfafa hadin gwiwar tsaro da kare fararen hula daga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ƴanbindiga.
Taron dai an yi shi ne da nufin tabbatar da cewa dukkan mabiya addinai za su iya gudanar da addininsu cikin aminci.
Hakan ya biyo bayan ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta, musamman saboda kisan kiyashin da ake zargin ana yi wa kiristoci, ikirarin da hukumomin Najeriyar suka musanta.
Amurka ta yi maraba da ƙoƙarin Najeriya na magance matsalar rashin tsaro, musamman a jihohin Arewa ta tsakiya.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ne ya jagoranci tawagar Najeriyar da ta ƙunshi ma’aikatu da hukumomi 10, yayin da mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka Allison Hooker ta jagoranci tawagar Amurka da ke da wakilaiu daga hukumomin tarayya takwas.
Sanarwar hadin gwiwa da aka fitar ranar Alhamis ta jaddada ƙudurin gwamnatocin biyu na tabbatar da ƴancin addini da kare ƴancin faɗin albarkacin baki da gudanar da taron lumana.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ‘’Tawagar ta Amurka ta godewa Najeriya kan matakan gaggawa da ta ɗauka na ƙarfafa tsaro ga al’ummomin Kirista da mabiyan sauran addinai da ke cikin haɗari sakamakon ayyukan ta’addanci.”
Ƙasashen biyu dai na musayar bayanan sirri domin tunkarar matsalar ta’addanci daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu a arewacin Najeriya.












