Haɗakar ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya ta Najeriya, (JOHESU) ta ce ‘yan Najeriya su ɗora wa gwamnatin tarayya alhakin wahalhalun da marasa lafiya da sauran masu buƙatar kulawar lafiya ke fuskanta sakamakon yajin aikin da mambobinta ke yi.
Ƙungiyar ta ce buƙatarta ɗaya tilo ita ce aiwatar da rahoton da ya shafi daidaita tsarin albashin ma’aikatan kiwon lafiya na CONHESS.
Sakataren JOHESU na ƙasar, Martin Egbanubi ne ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Ya ce duk da sanin tasirin yajin aikin a kan ƴanƙasa, bai kamata a ɗora musu laifi ba.
Ya ce, “Mun san irin tasirin da yajin aikin ke yi wa ‘yan Najeriya, amma bai kamata ‘yan ƙasa su ɗora mana laifi ba. Gwamnati ce ya kamata ta ɗauki alhaki, domin ita ce ke da haƙƙin yin abin da ya dace domin kauce wa irin wannan yajin aiki a nan gaba.”
Egbanubi ya ƙara da cewa JOHESU na fahimtar halin da marasa ƙarfi ke ciki, musamman waɗanda ba su da ƙarfin zuwa asibitoci masu zaman kansu, amma ya ce mambobin ƙungiyar ma suna shan wahala.
Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci masu kishin kasa su yi kira ga gwamnati ta gaggauta magance buƙatar domin dakatar da yajin aikin.











