Home Taska Dakarun Sojin Najeriya Sun kashe ƙasurguman ’Yan Bindiga Biyu a Zamfara

Dakarun Sojin Najeriya Sun kashe ƙasurguman ’Yan Bindiga Biyu a Zamfara

Zamfara

Dakarun Sojin Najeriya Sun kashe ƙasurguman ’Yan Bindiga Biyu a Zamfara

 

Dakarun rundunar Operation Fansan Yamma na sojin Najeriya sun kashe ƙasurguman ‘yan bindiga biyu tare da wasu mayaƙa bakwai a jerin hare-haren da suka gudana cikin kwanaki uku a jihohin Zamfara da Katsina.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar sojin, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya fitar.

Sanarwar ta ce a Jihar Zamfara, dakarun sansanin Bagega sun kai wani samame a Ƙaramar Hukumar Anka, inda suka kashe ‘yan ta’adda bakwai ciki har da manyan jagororinsu, Gomina da kuma Anaruwa, wanda ƙanin kwamandan ‘yan bindiga, Kachalla Idi Aiki.

A cewar Osoba, dakarun sun fara arangama da ‘yan ta’addan ne a kan hanyar Bagega zuwa Anka, lamarin da ya tilasta ’yan bindigar tserewa suka bar baburansa.

Sai dai daga bisani ‘yan ta’addan sun sake dawowa sansanin sojin domin daukar fansa, sai dai dakarun tare da haɗin gwiwar sojin sama sun fatattaki maharan, inda har aka samu nasarar kashe wasu uku daga ciki.

Bayanai sun ce dakarun sun ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu tare da harsasai da kuma babura bakwai.

A wani samamen da aka kai ranar 3 ga Mayu, dakarun sun sake hallaka wasu ‘yan ta’adda biyu a yankin, sai dai wani soja ya rasa ransa a filin daga.

Haka kuma, a Jihar Katsina, dakarun sansanin Fudma sun kashe ‘yan ta’adda tara ciki har da kwamandoji biyu a wata arangama da suka yi da su a kan hanyar Turare zuwa Yantumaki a Ƙaramar Hukumar Dutsinma.

Sanarwar ta ƙara da cewa an ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu da babura tara daga hannun ‘yan ta’addan a jihohin biyu.

Bugu da ƙari, dakarun sun kashe wasu huɗu tare da ƙwato bindigogi biyu, harsasai, wayoyin salula bakwai da kuma kuɗi Naira dubu 153.

Rundunar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin daƙile ayyukan ta’addanci.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga PantamiGazawar Demarketing: Yadda Sukar Rarara Mai Cike da Kiyayya ga Pantami Ya Rushe Daga Yushau A. ShuaibƘungiyar NARD ta yi Barazanar Shiga Yajin AikiDakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 Sun Ceto Mutane 9 da akai Garkuwa da suƳan Bindiga sun kai Hari a Kotun Shari'a da ke Jihar KatsinaBa ma Goyon Bayan a Riƙa Tura Sojoji Domin Aikin Tsaro a Lokacin Zaɓe - INECJam'iyyar NDC ta Buƙaci Sanata Hanga da Gaya da su Sake Tunani Kan Sauya SheƙaYan Bindiga Sun Kashe Kanal Abdussalam Ude Sun Raunata Matarsa
X whatsapp