Home Taska Samar da Tsaro: Sojojin Najeriya sun Kama ƴan ƙasashen Wajen 46

Samar da Tsaro: Sojojin Najeriya sun Kama ƴan ƙasashen Wajen 46

Soji

Samar da Tsaro: Sojojin Najeriya sun Kama ƴan ƙasashen Wajen 46

 

Sojojin Najeriya sun sanar da kama ƴan ƙasashen waje 46 a wani aikin samar da tsaro da suka gudanar a jihar Ogun da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar.

A cewar rundunar, an kai samamen ne a ranar Alhamis a yankunan Ijebu Imushin da Ijebu Ilese tare da wasu ƙauyuka da ke kusa, bayan samun bayanan sirri masu muhimmanci.

Mai magana da yawun rundunar, Idereghi Samuel Akari, ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen sun shafe kusan watanni shida a Najeriya ba tare da takardun izinin zama ba.

Ya ƙara da cewa mutanen sun shaida wa jami’an bincike cewa su ‘yan kasuwa ne da ma’aikata masu alaƙa da kamfanin QNET, wani kamfanin sayar da kayayyaki ta intanet mai hedikwata a Hong Kong.

Sai dai kamfanin QNET ya sha fuskantar zarge-zarge a Najeriya, inda hukumomi ke danganta kamfanin da damfara da safarar mutane da kuma shigo da mutane ba bisa ƙa’ida ba amma kuma kamfanin ya musanta hannu a irin waɗannan ayyuka, yana mai cewa yana nesanta kansa da masu amfani da sunansa wajen aikata laifi.

Kamen na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa a yammacin Afirka kan wasu ƙungiyoyin da ake zargi da amfani da sunan kamfanin wajen yaudarar mutane da alƙawuran samun aiki a ƙasashen waje da kuma samun kuɗi cikin sauƙi.

Daga cikin mutanen da aka kama, guda 18 ‘yan ƙasar Burkina Faso ne, 23 kuma daga Ivory Coast, huɗu daga Togo yayin da kuma mutum ɗaya daga Senegal ne.

Daga bisani, an miƙa waɗanda aka kama ga Hukumar Shige da Fice ta Najeriya domin ci gaba da bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga PantamiGazawar Demarketing: Yadda Sukar Rarara Mai Cike da Kiyayya ga Pantami Ya Rushe Daga Yushau A. ShuaibƘungiyar NARD ta yi Barazanar Shiga Yajin AikiDakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 Sun Ceto Mutane 9 da akai Garkuwa da suƳan Bindiga sun kai Hari a Kotun Shari'a da ke Jihar KatsinaBa ma Goyon Bayan a Riƙa Tura Sojoji Domin Aikin Tsaro a Lokacin Zaɓe - INECJam'iyyar NDC ta Buƙaci Sanata Hanga da Gaya da su Sake Tunani Kan Sauya SheƙaYan Bindiga Sun Kashe Kanal Abdussalam Ude Sun Raunata MatarsaMutane 15 Sun Mutu a Sabon Harin Yan Bindiga a Jihar Benue Zaɓen 2027: Uba Sani ya zaɓi MataimakinsaJami'an Tsaro Sun Kuɓutar da Mutane 32 Yayin da 4 Suka Mutu a Jihar Sokoto 
X whatsapp