Kungiyar malaman kwalejojin ilimi ta tarayya Nijeriya COEASU ta jingen yajin aikin da take har na tsaho kwanaki sittin (60).
Shugaban kungiyar reshen kwalejin ilimi ta tarayya dake Kano Comrade Ado Muhammad Abdullahi ne ya shaida hakan ga Jaridar PRNigeria Jim kadan bayan fito daga taron kungiyar na kasa kan yajin aikin da kwangiyar ta kwashi makwannin tana yi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Comrade Abdullahi Muhammad yace sun jingine yajin aikin na tsahon kwanakin samakon, sauraren koken su da Gwamnatin tarayya Nijeriya tayi wannan ya sanya su bata damar domin ganin matakin da zata dauka.
Ana dai kallon wannan mataki kungiyar ta COEASU matsayin wata hanya ta shawo kan matsalar dake tsakanin ta da Gwamnatin tarayyar kasar.
Sai dai kuma ba wannan ne karon farko da kungiyar ke tsunduma yajin aiki ba, daga bisani su gindaya wasu sharruda da gwamnatin tarayyar kasar; ko da yake dai kungiyar tun da fari ta bayyana cewa gwamnatin ta kasa cika mata Alkawarin data dauka tun da fari.











