Home DUNIYA Ana Cigaba da Aikin Ceton Wadanda Gada ta Rufta Dasu a Kasar...

Ana Cigaba da Aikin Ceton Wadanda Gada ta Rufta Dasu a Kasar India

Rahotanni na bayyana cewa ana cigaba da laluben wadanda suka nutse a ruwa bayan ruftawar wata tsohuwar gada a kasar India, abinda ake ganin ya shafi akalla mutane 130.

Tun da fari dai ‘Yan sanda a kasar sun tabbatar da mutuwar mutane fiye da 130, lokacin da wata gada da ta kwashe shekaru sama da 100 ana amfani da ita ta rushe, abinda ya sanya wasu da dama  fadawa ruwa.

Daya daga cikin manyan jami’an ‘yan sanda a kasar ta India, Ashok Kumar Yadav, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar zuwa wayewar garin Litinin din nan, adadin mutane 132 aka tabbatar da mutuwarsu bayan rushewar gadar da ta kwashe kusan shekaru 150 ana amfani da ita.

Ministan dake kula da Yammacin jihar Gujerat, Brijesh Merja yace kuma anyi nasarar ceto mutane sama da 80 da ransu.

Mahukunta sun ce akalla mutane kusan 500 ke kan gadar lokacin da ta rufta sakamakon sakewar da robobin dake rike da ita suka yi, cikin su harda mata da yara.

Ita dai wannan gadar ba’a dade da kammala gyaranta ba, tana garin Morbi ne dake da nisan kilomita 200 daga Ahmedabad a Jihar Yammacin Gujerat.

Kafofin yada labaran kasar sun ce mutanen da suka taru akan gadar suna gudanar da ibada ne akan kogin Machchhu, yayin da wasu kafofi suka nuna hotunan bidiyon da ake bayyana cewar na hadarin ne dauke da mutanen dake kokarin yin fito domin tsira da rayukansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp